Kamfanin Dillancin Labarun Palasdinu ya fada a yau alhamis cewa; Dan jarida na bayan nan da ya yi shahada shi ne Ramy Rayyan a wani harin da sojojin sahayoniya su ka kai wa yankin Basdhat da ke gabacin Gaza. Wannan ya sa adadin ‘yan jaridar da su ka yi shahada a tsawon lokacin yaki zuwa ‘yan jarida bakwai. Daga cikin ‘yan jaridar da su ka yi shahada da akwai wata mace mai suna Najlaa Mahmud Alhaj. Kawo ya zuwa yanzu jumillar palasdinawan da su ka yi shahada sun kai 1364, yayinda wadanda su ka jikkata su ka kai 7680. ABNA
31 Yuli 2014 - 08:08
Lambar labari: 627912
Yakin da H.K Isra’ila ta shelanta akan Gaza ya ci rayukan ‘yan jarida bakwai.